Yau Kwankwaso Da Kwankwasawa Zasu Fice Daga APC


Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai ci, Rabi’u Musa Kwankwaso zai gana da magoya bayansa na darikar Kwankwasiyya a daren yau don tattauna batun ficewarsa tare da dubban magoya bayansa da ke a ko’ina a fadin kasar na daga jam’iyyar APC

Tun ba yau ba ne dai Kwankwasawa ke ta yin kiraye-kiraye ga madugunsu da fice daga jam’iyyar APC sakamakon hanasu rawar gaban hantsi da mabiya darikar Gandujiyya ke yi a jihar Kano tun bayan da dangata ta yi tsami tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Rahotanni na nuna cewa dama dai Kwankwaso ya shirya bayyana ficewa daga jam’iyyar APC a ziyarar da ya nufi yi a ranar 30 ga watan Janairu, wanda ala dole ya soke ziyarar sakamakon al’amura na tsaro da jami’an tsaro suka ce zuwan nasa ka iya gurbatawa


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like