Yau Ce Ranar Masu Buƙata Ta Musamman Ta Duniya


Majalisar ɗinkin duniya ce ta ware kowacce ranar 3 ga watan Disamban kowacce sheƙara domin bikin ranar wanda ke mai da hankali wajen wayar da kan al’ummar duniya domin tallafawa masu buƙata ta musamman, samar da nagartattun hanyoyin da za su tallafa musu, har da ma ƙoƙarin nusar da hukumomi don samar da daidaito wajen damawa da su a cikin dukkanin al’amuran mutane.

Kimanin mutane biliyan ɗaya ne a faɗin duniya ke rayuwa da nau’o’in tawaya ko naƙasu a jikinsu. Adadin da ya kai kaso goma sha biyar cikin ɗari (15%) na mutanen duniya.

Taken bikin ranar ta bana shi ne: Samarwa ko koyawa masu buƙata ta musamman ayyukan yi ko sana’o’i, tabbatar da samar musu da gurabe a harkar tafikar da al’amuran al’umma, da ma samar musu da daidaiton damarmaki a tsakanin al’umma.

Wanda idan akai hakan zai basu damar neman ilimi, koyar sana’o’i da kuma damawa da su a dukkan harkokin rayuwa domin a rage musu dogaro ga mutane, sannan a magance matsalar barace-barace da ta addabi musamman arewacin ƙasarnan.

Sai dai akwai buƙatar gwamnatoci, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya da su tsaya tsayin daka domin samar da hanyoyin da za su daƙile afkuwar larurorin da ke saurin naƙasa mutane, sannan a samar da isassun ma’aikatan lafiya musamman a matakin farko.

Sashin likitancin Fisiyo da ke kula da matsalolin jijiya, ƙashi da tsoka na da muhimmiyar rawar takawa a bikin wannan rana, saboda jiɓantar kula da larurorin da suka fi naƙasa mutane da sashin ke da shi.

Samar da isassun likitocin Fisiyo a ɗaukacin asibitocin ƙananan hukumomi da asibitocin da ke ƙarƙashin hukumar lafiya matakin farko zai rage yawaitar samun mutane masu naƙasa da kaso mai tsoka.

SpecialKids

#PersonsWithSpecialNeeds

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like