Yaro mai shekaru uku ya kamu da cutar Korona a Imo


An samu wani yaro mai shekaru uku da ya kamu da cutar Korona a jihar Imo a cewar, Farfesa Maurice Iwu shugaban kwamitin kar-ta-kwana na yaki da cutar Covid-19 a jihar.

Da yakewa yan jaridu jawabi ranar Laraba a Owerri babban birnin jihar, Iwu ya ce an killace mutane bakwai daga cikin masu fama da cutar a cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya dake Owerri.

Ya ce wasu iyali su shida da suka hada da uba da kuma uku daga cikin yayansa ciki har da yaro dan shekara uku an gwada su suna dauke da cutar.

Ya kara da cewa za a bawa yaron kulawa ta musamman.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like