Yaro mai shekaru 9 ya fada rijiya ya mutu a Kano


Wani yaro dan shekara 9 mai suna Halliru Abdullahi ya mutu bayan da ya fada rijiya a unguwar Kofar Kudu dake garin Gaya a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Sa’idu Muhammad ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9 na safe.

Ya ce marigayin yana wasa tare da abokansa a bakin rijiyar lokacin da lamarin marar dadi yafaru.

“Mun samu kiran kai daukin gaggawa daga mai unguwa Hamza Abdullahi da misalin karfe 9:00 na safe inda yace wani yaro ya fada rijiya

“Da samun kiran munyi gaggawar tura jami’an ceto zuwa wurin da misalin karfe 09:40.

“An samu nasarar ceto Abdullahi, baya cikin hayyacinsa inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

“An mikawa mai unguwa Abdullahi Hamza gawarsa,”a cewar Muhammad.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like