Yaro dan shekara 7 ya fada rijiya ya mutu


Hukumar kashe gobara ta jihar Kano,ta ce wani yaro mai shekaru 7 ya mutu bayan da ya fada rijiya a layin Yarabawa dake Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni dake jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sa’idu Muhammad ya fitar a ranar Laraba.

Muhammad ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da yaron yaje ɗibar ruwa.

“Mun samu kiran kai ɗaukin gaggawa daga Abdularauf Abba da misalin karfe 06:00 na yamma da samun labarin munyi gaggawar tura jami’an mu na aikin ceto inda suka isa da karfe 06:07.”

“An ciro gawar yaron daga cikin rijiyar aka kai ta asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda aka tabbatar da mutuwarsa,” ya fadawa kamfanin dillancin labarai na NAN.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like