Yaro dan shekara 16 ya mutu a kududdufi a Kano


Wani yaro mai suna,Shahid Lawal ya nutse a ruwa ranar Alhamis lokacin da yake wanka cikin wani kududdifi dake unguwar Bachirawa Ramin Kasa a karamar hukumar Fagge ta jihar.

A wata sanarwa ranar Juma’a dake dauke da sahannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, Saidu Muhammad, ya ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis da yamma lokacin da marigyin yaje wanka.

Muhammad ya ce “Mun samu kiran kai daukin gaggawa daga Rabi’u Nasiru da misalin karfe 06:23 na yamma dake cewa an hangi gawar Lawan na yawo akan ruwan kududdufi.

” Da samun labarin munyi gaggawar tura jami’an mu inda suka isa wurin da misalin karfe 06:34.

“An samu Lawan ya mutu aka kuma mika shi hannun, Alhaji Rabi’u Bala dagacin Bachirawa Gabas.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like