Wata yarinya yar shekara 17 da ta fito daga birnin Texas na Amurka ta shiga kundin tarihi na duniya da ake kira Guiness World’s Record a matsayin mace mafi tsawon kafa da kuma matashiya mafi tsawon kafa.

Matashiyar yarinyar mai suna,Maci Currin ta kafa tarihin ne bayan da awon da aka yi ya nuna kafarta ta dama na da tsawon 135.267cm a yayin da ta hagu take da tsawon 134.3

Duk da cewa tsayin nata yana bata kalubale kamar a cikin gida da kuma wajen kayan sawa a wani bangaren yana bata wasu damarmakin kamar wajen wasanni inda take bugawa kungiyar Volley Ball ta makarantarsu