Yara miliyan takwas na cikin garari | Labarai | DWA cikin wani rahoton da ya fitar a wannan Alhamis, asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” ya ce a cikin kasashe 15 ne matsalar ta fi kamari inda kananan yaran ke cikin halin ni ‘yasu saboda rashin wadataccen abinci, sai dai rahoton ya kuma bayyana hudu daga cikin kasashen da suka hada da Afghanistan da Ethiopia da Haïti da Yémen da a matsayin wadanda barazanar ta fi daukar hankali da muni a wannan shekara.

Wasu daga cikin dalilan da asussun ya ambata  da ke zama musabbabin barazanar su ne matsalar fari sakamakon karancin ruwan sama, da canjin yanayi da illolin da annobar corona ta haifar da kuma tashin-farashin kayan abinci da duniya ke fuskanta a yanzu sakamakon mamayar Ukraine take fusknata daga makwabciyarta Rasha.
Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-1
66 shares, -1 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg