Yara da yawa sun makale a wani ginin bene mai hawa uku da ya ruguzo a Lagos


Wani ginin bene mai hawa uku dake yankin Itaa-Faaji a jihar Lagos ya ruguzo inda ya danne yara yan makaranta masu yawan gaske.

Wani shedan gani da ido ya fadawa jaridar The Cable cewa lamarin yafaru ne da misalin karfe goma na ranar Laraba. Daya daga cikin hawan benen ana amfani da shi ne a matsayin makaranta kuma yara dalibai na tsaka da karatu lokacin da ginin ya rufta.

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos da sauran ma’aikatan ceto na can suna aikin ceto yaran dama sauran mutanen da suka makale.

An garzaya da wasu daga cikin yaran da aka samu nasarar zakulo su daga cikin baraguzan ginin.

Faduwar gini irin haka abune da ya zama ruwan dare a Najeriya kuma da alama hukumomi sun gaza daukar mataki da zai kai ga shawo kan faruwar lamarin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like