‘Yar Shekaru 17 Ta Kashe Mutumin Da Ya Yi Yunkurin Yi Mata FyadeAn gurfanar da wata matashiya mai shekaru 17 a gaban kuliya a sakamakon kashe wani saurayi da ya yi yunkurin yi mata fyade a kasar Afrika ta Kudu.

Rahotanni sun bayyana cewa saurayin mai shekaru 21 ya farwa matashiyar ne yayin da take kan hanyar ta ta zuwa wani guri da ba a bayyana ba, inda suka fara kokawa har ta ci karfinsa,ta daba masa wuka.

Bayan da aikata abun ne ta mika kanta ga ‘yan sanda.

‘Yan sanda sun bayyana cewa lokacin da ta mika kan na ta, tana cikin rudani. 
A don haka ana bata duk wata kulawa da ya kamata.

Haka kuma sun ce ba za su bayyana sunan taba saboda a karkashin dokokin kasar, har yanzu yarinya ce karama.

Kotun za ta kara sauraran karar a yau, 15 ga watan Yuni, inda matashiyar za ta fada wa kotun cewa, abun da ta aikata ta yi ne domin ta kare kanta.

Ita kuwa kotun zata dora maganar ta ta akan mizanin shari’a ta yanke hukunci.

Fyade dai ya na daya daga cikin abubuwan da ke ciwa mutanen Afrika ta Kudu tuwo a kwarya, inda ake samun fiye da 60,000 a kowacce shekara.

Da yawa a cikin matan na rasa rayukan su a sakamakon haka.

Comments 0

Your email address will not be published.

‘Yar Shekaru 17 Ta Kashe Mutumin Da Ya Yi Yunkurin Yi Mata Fyade

log in

reset password

Back to
log in