Yanzu-Yanzun Nan: Ba Mu Tattara Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2019 A Yanar Gizo Ba – Farfesa Mahmoud Yakubu.


Shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa, INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya yi bayanin a kan dalilin da ya hana hukumar tura sakamakon zabe yanar gizo, sabanin abin da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar, ke ikirari.

Wannan jawabi ya bayyana a kotun amsar korafe-korafen zabe ne da safiyar Talata a Abuja, inda lauyan shugaba Muhammadu Buhari, Alex Izinyon, S.A.N, ya kunna wani faifan bidiyo wanda ke nuna shugaban INEC yana bayanin dalilin da ya hana hukumar amfani da yanar gizo.

Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi bayani a faifan bidiyon cewa hukumar ta gaza yin amfani da yanar gizo wajen tattara sakamakon zabe ne saboda karancin na’urorin sadarwa da tsoron yan zambar yanar gizo.

Bugu da kari, lauya Izinyon ya gabatar da wani bidiyon daban wanda ke dauke da hirar farfesa Mahmoud Yakubu da wani dan jarida inda ya yi bayani filla-filla kan kalubalen da ke tattare da tura sakamakon zabe yanar gizo.

Kotun ta amince da wannan shaidu biyu.

A ranar Litinin, 15 a Yuli, kotun zaben shugaban kasa ta tabbatar da faifan bidiyoyi 48 da jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, ya gabatar mata kan magudin zaben da ya gudana a lokacin zabe.

Atiku da jam’iyyarsa na kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 23 ga Febrairu da ya gudana wannan shekarar.

Koya kuke kallon wannan dambarwa?


Like it? Share with your friends!

1

Comments 2

Your email address will not be published.

  1. Ni a ganina da Atiku ya hakura da Shari’ar ya dawo ya had a kai da Shugaban Kasa dan Gina kasar yafi, dan mu nuna goyon bayan aikine ba raba kai ba.

  2. Write a comment *Sakamakon ganin sahihancin zaben daya gabata ne yasa aka bama GMB ticket din cin zabe da wuri, Don haka ina kira ga kotun koli da tayi gaggawar rufe wannan case din.

You may also like