Yanzu haka shugabannin PDP na zanga-zanga a hukumar INEC


A yanzu haka shugabannin jam’iyyar PDP na kasa na can na gudanar da zanga-zanga a ofishin hukumar zabe ta kasa INEC dake Abuja kan zaben shugaban kasa da ya gudana.

Shugaban jam’iyyar PDP,Uche Secondus shine ya jagoranci dubban magoya bayan yan jam’iyyar ya zuwa ofishin hukumar dake unguwar Maitama.

Atiku Abubakar dan takarar jam’iyar a zaben shugaban kasa ya yi rashin nasara da tazarar kuri’u sama da miliyan uku kan abokin takararsa na jam’iyar APC wato shugaban kasa Muhammad Buhari.

Amma jam’iyar tayi watsi da sakamakon da ta ce yana cike da kura-kurai.

A yanzu haka shugabannin jam’iyyar na hedkwatar hukumar zaben inda suke yin wakokin nuna goyon baya.


Like it? Share with your friends!

4
74 shares, 4 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like