Yansanda sun kama wani da kokon kan mutum


Jami’an ƴansandan birnin tarayya Abuja sun kama wani mutum,Valentine Ezeogu mai shekaru 38 inda ake zarginsa da mallakar kokon kan mutum.

Kwamishinan ƴansandan birnin,Bala Chiroma shine ya bayyana haka lokacin da yakewa yan jaridu bayyani kan aiyukan rundunar.

Chiroma ya ce an kama mutumin da ake zargin ne ranar 8 Janairu lokacin da jami’an rundunar suke gudanar da sintiri kusan da rukunin gidaje da ake kira Finance Quarters dake yankin Wuye biyo bayan tsegumin da suka samu.

Ya ce mutumin da ake zargi wanda ya ce shi mai kula da lambu ne kuma yana rayuwa ne a wani gida da ba a kammala ba,an same shi da kokon kan kunshe a cikin leda da kuma wasu kayan tsare-tsafe.

Chiroma ya ce za a gurfanar da mutumin da ake zargi a gaban kotu da zarar kammala bincike.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like