Yanbindiga sun yi garkuwa da wani lauya a Osun


An rawaito wasu yanbindiga sunyi garkuwa da wani lauya,Mista Musbahu Adetumbi a Iwaraja dake jihar Osun.

Lauyan mazaunin, Ibadan na kan hanyarsa ne ta zuwa Akure domin halartar zaman kotun daukaka kara lokacin da aka yi garkuwa da shi da maraicen ranar Litinin.

Mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi NBA reshen jihar Ibadan, Ibrahim Lawal ya tabbatar da sace Adetumbi.

Ibrahim ya ce “mummnun labarin sace abokin aikinmu, Musibau Adetumbi ya girgiza mu. Yana kan hanyarsa ne ta zuwa Akure daga Ibadan tare da wasu lauyoyi biyu.Musibau kadai da kuma direban motarsa kirar Honda Civic aka sace.”

Ibrahim ya ce masu garkuwa sun budewa motar wuta a Iwaraja dake Osun abin da ya tilasta musu tsayawa inda suka dauke shi tare da direban.

Ya kara da cewa masu yanbindiga sun kyale lauyoyi mata biyu dake tare da su inda ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar an sako lauyan tare da direban sa.


Like it? Share with your friends!

2
64 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like