Yan takara 41 ne ke neman zama gwamnan Lagos


Hukumar zabe ta kasa INEC a jihar Lagos ta wallafa cikakken bayanin yan takara 41 na jam’iyu daban-daban dake neman darewa kujerar gwamnan jihar.

A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, yan takara 589 daga jam’iyu daban-daban ke neman cike gurbin kujeru 40 dake majalisar dokokin jihar.

Wallafa sunayen da aka yi na ranar Juma’a ya nuna cewa jam’iyu 41 cikin 62 da ake da su a jihar ne za su fafata a neman lashe zaben kujerar gwamnan jihar ya yin da jam’iyu 47 za su shiga zaben kujerar majalisar dokokin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta INEC a jihar Lagos,Femi Akinbiyi ya bayyana cewa wallafa sunayen na nufin cewa hukumar ta shiyar tunkarar zaɓen 2019.


Like it? Share with your friends!

-2
61 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like