Rahotanin da ke fitowa daga arewacin jahar Tahoua a jamhuriyar Nijer su na nuna cewa a ranar 1 ga watan mayun nan da muke ciki, an wa rundunar askarawan kasar da ke yawon sintiri a yankin Tilliya na Garde Nationale du Nijer wajajen garuruwan Ekenewane da Intazey kwantan bauna wajan karfe 5:20 na yamma.

Wadansu mutane ne a kan babura sama da 100 dauke da makamai da ba a fayyace su ba, suka abkawa rundunar inda suka hallaka soja 16, suka kuma yi awon gaba da motoci 2, suka lalata mota daya.

Sojoji 6 sun raunata kuma suna assibitin Tahoua. Su kuwa sojojin kasar, sun hallaka da yawa daga cikin maharan da kuma lalata kayan su na yaki suka tsere da su daga bisani.

Ana kyautata zaton yan tsaurin kishin addinin islama ne da ke kutsowa a wannan iyakar ta Nijer da Mali suka aikata wannan danyen aiki. A baya su na abkawa fararen hulla ne kawai, sai gashi yanzu sun wa askarawan kasar wannan kwantan bauma.

Saurari cikakken rahoton a sauti: