Wasu yan ta’adda da ba’asan ko suwaye ba sun kashe farar hula 16 a wani hari da suka kai arewacin Burkina Faso.

A cikin wata sanarwa ranar Laraba gwamna, Salfo Kabore ya ce masu tsattsauran ra’ayi sun kai hari a ranakun Asabar da Lahadi kan kauyen Pobe Mengao a lardin Soum dake iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Tun da farko makonnan mazauna yankin sun kai rahoton faruwar harin ga kafafen yada labaran kasar amma sai ya zuwa ranar Laraba da safe sannan jami’an gwamnati suka tabbatar da faruwar lamarin.

Yankin arewacin kasar Burkina Faso dake da iyaka da jamhuriyar Nijar da Mali ya zama wata mafaka ga masu tsattauran addinin musulunci wadanda suke yawan kai hare-hare kan fararen hula.