‘Yan Ta’adda Sun Karkashe’Yan Sanda Masu Yawa A Zamfara!


‘Yan sandan Nijeriya sun ce jami’ansu 16 ne suka mutu a jihar Zamfara bayan wata arangama da suka yi da barayin shanu a karamar hukumar Birnin Magaji ranar Alhamis din da ta gabata.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce ta ceto ‘yan sanda 20 daga hannun barayin shanun, sannan ta kashe barayi 104.

Sanarwar, wacce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya aike wa manema labarai ranar Talata da daddare ta kara da cewa jami’an tsaron sun kuma rusa sansanoni uku na barayin, sannan suka kwato shanu sama da 500 da awaki 79.

“An aike da jiragen helikwafta uku wadanda suka kaddamar da hare-hare a maboyar barayin shanu da sauran ‘yan fashi da makami da zummar kawar da gyauron su.

“Kazalika an aike da jami’an ‘yan sanda na musamman da wadanda ke yaki da ta’addanci da kuma wadanda ke yaki da ‘yan fashi da makami jihar ta Zamfara,” in ji sanarwar.

‘Yan sanda sun kashe ‘barayin shanu’ 100 a ZamfaraKotu ta daure shugaban UBE a Zamfara shekara 41Buhari ya ce da gangan APC ta tauye hakkin masu son yin takara

Lamarin dai ya faru ne da yammacin Alhamis din nan, yayin da jami’an ‘yan sanda na musamman ke sintiri a cikin dazuzzukan jihar ta Zamfara domin zakulo barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ke addabar sassan jihar da dama.

Haka kuma dakarun na musamman sun kama sama da mutum 85 da ake zargin gungun masu aikata miyagun laifuka ne a jihar.

Sanarwar ta ce an kuma kwato bindigogi kusan 80 da kuma wasu muggan makamai.

Sakamakon kwanton baunar dai rundunar ‘yan sandan kasar ta tura babban mataimakin sufeto janar domin zama babban kwamandan dakarun na musamman.

Babban aikin kwamandan shi ne maido da zaman lafiya a duka fadin Zamfara.

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.

A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala’i ga jihar Zamfara, Gwamn


Like it? Share with your friends!

1
73 shares, 1 point

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like