Yan shi’a sun sake arangama da jami’an tsaro a Abuja


Mambobin kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da aka fi sani da shi’a sun sake yin arangama da jami’an yan sanda a birnin tarayya Abuja.

Yan shi’ar da suka yi arangama da jami’an tsaro ranar Talata a harabar majalisar kasa sun sake bazama kan titunan birnin tarayya Abuja a yau Alhamis.

Dauke da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce inda suke wakokin kin jinin gwamnati, masu zanga-zangar sun bukaci da a gaggauta sako jagoransu Ibrahim Elzakzaky.

Sun tattaru a wajen harabar ginin sakatariyar gwamnatin tarayya inda suka yi jerin gwano ya zuwa dandalin Eagle Square lokacin da jami’an yan sandan kwantar da tarzoma suka tare su.

Wani shedar ganin da ido ya shedawa jaridar The Cable cewa rikici ya fara ne lokacin da yan sanda suka nemi suyi magana da jagororin zanga-zangar, sun kama mutane biyu da suka fito Nura Marafa da Mujahid Muhammad.

Jin haushin kama jagororin nasu yasa suka fusata har ta kai sun farma jami’an tsaron inda su kuma suka mayar da martani da harbi da kuma hayaki mai sa hawaye.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like