‘Yan Shi’a Sun Kira Taron Hadin Kan Musulmai A Abuja


Cikin satin daya gabata Mabiya Shi’a Almajiran Shaik Zakzaky suka shirya wani babban taro a Abuja na tsawon kwanaki biyar wanda suka kira shi da sunan ‘Makon Hadin Kai’ wanda suka gayyaci manyan Malaman Addinin Islama da masana daga bangarori daban daban suka gabatar da jawabai a wajan.

Taron wanda shine karo na 16 sun saba shiryawa ne duk lokacin da al’ummar Musulmai ke gudanar da bukukuwan tinawa da Maulidi inda suka masa take da “Son Manzon Allah Sirrin Hadin Kai” anyi taronne daga ranar 12 zuwa 17 ga watan Rabiul Auwal.

Cikin Manyan Malamai da suka halarci taron akwai Shaik Yahaya Sufi Babban Malamin Darikar Tijjaniya dake garin Bauchi da Shaik Khidir Lawal wanda ya wakilci Dr Khalid Abuja, Farfesa Dahiru Yahaya daga Jami’ar BUK dake Kano, da sauran Malamai daban daban daga mabanbantan mazhabobin Musulunci.


Like it? Share with your friends!

-1
85 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like