Yan Shi’a Sun gurgunta Harkokin Babbar Sakateriyar Birnin Tarayyar Abuja


A yau ne, ‘yan Shi’a suka mamaye yankin Babbar sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja inda suka gurgunta harkoki sakamakon zanga zangar da suke yi na neman gwamnati ta sako Shugabansu, Malam Ibrahim El Zakzaky.

Rahotanni daga Abuja sun nuna cewa ‘yan Shi’ar sun mamaye hanyoyin da ke yankin sakatariyar wadda ke kusa da fadar Shugaban kasa da kuma majalisar tarayya, lamarin da ya janyo ‘yan sanda suka yi amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga zanga.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like