Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Legas


Mambobin kungiyar nan ta #Revolutionnow dake kira a gudanar da juyin juya hali a Najeriya sun gamu da fushin jami’an tsaro bayan da suka fara taruwa a filin wasa na kasa dake birnin Legas gabanin su fara zanga-zanga.

Jami’an tsaro da suka hada da sojoji,yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su.

Masu zanga-zangar da suka fara isa filin da misalin karfe 7 na safe sun iske jami’an tsaro a kofar shiga filin wasan.

Wani daga cikin masu zanga-zanga ya fadawa manema labarai cewa suna tsaka da tsara yadda zanga-zangar zata gudana ne sai jami’an tsaron suka far musu.

Kwanaki biyu da suka wuce jami’an tsaron farin kaya suka kama Omoyele Sowore wanda shi ne ya shirya zanga-zangar

Wani jami’in tsaro ya ce sun samu umarni daga babban sifetan yan sanda na kasa kan suyi duk me yi yuwa wajen murkushe masu zanga-zangar.


Like it? Share with your friends!

-1
64 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like