Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum daya a harin kunar bakin wake a jihar Borno


Yan sanda a jihar Borno sun tabbatar da mutuwar mutum guda a wani harin kunar bakin wake da aka kai yankin Post Office dake birnin Maiduguri a karshen mako.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Edet Okon cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce , ranar Asabar da misalin karfe 7:15 na dare dan kunar bakin waken namiji dake kan hanyarsa ta zuwa Kasuwar Monday, da ya hangi tarin yawan jami’an tsaron da aka girke a wajen gidan mai na Oando dake yankin Post Office a cikin kwaryar birnin sai ya yi gaggawar tayar da bom din dake sanye a jikinsa inda ya kashe kansa shi kaɗai.

“Rundunar yan sandan jihar Borno ta tura jami’anta na sashen kwance bam domin tabbatar da cewa yankin baya dauke da wani abu da zai kawo cuta ga jama’a,” ya ce.


Like it? Share with your friends!

-1
117 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like