Yan sanda sun kwato shanu 36 daga hannu barayin shanu a Zamfara


Rundunar yan sandan jihar Kebbi, ta karbo shanu 36 daga hannun barayin shanu a jihar Zamfara a cewar kwamishinan yan sandan jihar,Garba Danjuma.

Danjuma ya fadawa manema labarai ranar Lahadi a birnin Kebbi cewa wasu daga cikin barayin an kama su tare da shanun ya yin da wasu suka tsere.

“Jami’an mu masu bincike sun tafi daga Birnin Kebbi zuwa Zamfara domin karbo shanun bayan da wasu mutane biyu, Abubakar Juli da Alhaji Ardo daga kauyen Asarara sun kai rahoton sace shanu 43 ranar 10 ga watan Satumba.

“Bayan cikakken bincike ma’aikatan mu sun kama, Abubakar Umar da Attahiru Sani daga kauyen Daki Takwas a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara bayan da aka same su da mallakar shanu 36 na sata,”

“Sauran mutanen da ake zargi da satar shanu sun samu nasarar tserewa amma muna bin sawunsu kuma nan ha dadewa ba zamu kama su,” ya ce.

Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-1
79 shares, -1 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg