Yan sanda sun kwato bindigogi 177 a Sokoto, Kebbi da Zamfara


Bindigogi dari da saba’in da bakwai yan sanda suka kwato a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara a kokarin da ake na kakkabe batagari a yankin.

Bashir Musa jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Najeriya shiya ta 10 dake da hedkwata a Sokoto shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Musa ya ce bindigogin da aka samu sun hada da Ak-47, mashin gan, fistol, bindiga kirar GPMG bindiga kirar gida da sauransu.

Ya ce shirin yin afuwa ga yan bindiga a jihar Zamfara ya taka muhimmiyar rawa wajen samo bindigun.

A cewar mai magana da yawun rundunar, yansandan sun samu nasarar gano wani rumbun ajiye makamai na shararren dan bindiga da ake kira Zakuri a jihar Zamfara inda aka samu bindiga kirar Ak-47 guda 30.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like