Yan sanda sun kashe wasu matasa biyu a Kano


An zargi jami’an yan sanda da kashe wasu matasa biyu, Ibrahim Isa wanda aka fi sani da Banufe da kuma Ibrahim Sulaiman wanda ake kira da Mainasara a unguwar Sharada dake Kano.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da karfe 11 na dare a rumfar wani mai sayar da Indomie dake kusa da babban masallacin Juma’a na Sharada.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsaniya ta barke a wurin da bayan da Mainasara ya bukaci dalilin da yasa jami’an tsaron suka zo kama kaninsa mai suna Gaddafi

Daya daga cikin yan sandan mai suna Ado shi ne yayi kokarin jawo Mainasara daga cikin shagon har ta kai ga ya caka masa wuka har sau biyu inda ya fara zubar da jini nan take.

Kokarin da mutane su kai na kawo masa dauki ya sa jami’an yan sanda harbi inda aka samu Banufe kuma ya mutu nan take.


Like it? Share with your friends!

1

You may also like