Yan Sanda Sun Kashe Wani Mutum Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami, Suka Kuma Kama Mutane Biyu 


Yan sanda a jihar Adamawa a ranar Talata sun ce sun dakile wani shirin yin fashi a tsohuwar GRA Jimeta inda suka kashe mutum daya suka kuma samu nasarar kama biyu. 

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Othman Abubakar, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Yola  cewa  rundunar ta samu kiran kai daukin gaggawa da misalin karfe 1:00 na dare daga wani Alhaji Bakari,inda yace yan fashi sun shigar masa gida.

“Da muka samu kiran sai  muka tura jami’anmu dake bangaren yaki da fashi da makami inda suka killace yankin.

   ” Da suka hangi mutanen mu sai suka bude wuta inda a musayar wutar aka kashe daya daga cikinsu aka kuma kama biyu,”Abubakar yace. 

 Yace rundunar baza ta sassauta ba har sai mutane sunyi bacci idonsu biyu a rufe. 

Mai magana da yawun rundunar ya shawarci jama’a da sukai rahoton duk wani motsin mutane da basu amince dashi ba ga ofishin yan sanda mafi kusa dasu. 

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like