Yan sanda sun kama yan fashi da makami 8 a jihar Osun


Jami’an rundunar yan sanda ta musamman dake yaki da yan fashi da makami wacce aka fi sani da SARS sun samu nasarar kama wasu mutane 8 da ake zargi da aikata fashi da makami a jihar Osun.

Da da take magana da manema labarai kwamishiniyar yan sandan jihar,Abiodun Ige ta ce wadanda ake zargi sun hada da Oyewunmi Oyelakin, Adebayo Yemi, Adeyeye Opeyemi, Olawale Munirudeen, Sunday Ogbemudia, Lasisi Isiaka, Samuel Johnson and Isiaka Fatai.

Kwamishiniyar ta ce “Mun kama wasu da ake zargi yan fashi ne da suka dauki tsawon lokaci suna addabar al’ummar Osun.Mun samu damar bibiyar ayyukansu tun daga shekarar 2018 kuma mun samu nasarar kama dukansu,”

Ta ce motoci biyar, wayoyin hannu,Laptops, agogon hannu da sauran kayayyaki da aka kwace daga masu su a wuraren daban-daban da kuma bindiga da harsashi aka samu a wurinsu.


Like it? Share with your friends!

1
70 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like