Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da laifin yi wa mahaukaciya fyade


Rundunar yansandan jihar Anambra ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da haikewa wata mahaukaciya mai shekaru 23 wacce aka sakaya sunanta.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa matar ta fito ne daga yankin Ezi Umunya a karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra.

Mutane biyun da ake zargi da aikata fyaden Okwuchukwu Anyanwu da Emeka Odoh, sun yi amfani da damar kasancewar ta mahaukaciya wajen aikata lalatar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yansandan jihar Anambra, Haruna Muhammad ya ce za a gurfanar da mutanen gaban kotu da zarar an kammala bincike.


Like it? Share with your friends!

1
87 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like