Yan sanda sun kama mutumin da ya yi garkuwa tare da kashe yaro dan shekara 17


Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wani matashi da ya kashe wani yaro dan shekara 17 bayan da yayi garkuwa da shi kafin daga bisani ya binne shi a gonarsa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa shi ne ya sanar da kama matashin lokacin da suka tasa keyarsa zuwa wurin da ya binne gawar a gonarsa.

Matashin mai suna Anas Saidu mazaunin garin Hayin Gwarmai ne dake karamar hukumar Bebeji ta jihar ya kuma yi garkuwa tare da kashe Tijjani Kabiru.

Matsalar garkuwa da mutane abu matsala ce da ta zama ruwan dare a y a yankin arewacin Najeriya


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Allah yaji qan wanda aka kashen, yayi masa rahma, su kuma masu wannan aika-aikan allah ya shiryar dasu, wanda ba masu shiyuwa bane, ya allah bayinka ne, kai ka san yadda zaka yi dasu.

You may also like