Yan sanda sun kama Mompha


Jami’an yan sandan kasa da kasa a birnin Abuja sun kama Isma’il Mustapha da aka fi sani da Mompha.

Mompha wanda ya shahara a kafar sadarwar zamani ta Istagram inda yake nuna yadda yake rayuwa cikin daula da kuma jin dadi.

Matashin na zaune ne birnin Dubai inda yake sana’ar canjin kudi a zahirance amma a badini kuma gawurtaccen danfara ne.

Ruwa ya kare masa bayan da hukumar yan sandan kasa da kasa wato Interpol ta yi kokarin kama shi a birnin Dubai bayan da aka zarge shi da zanbar kudi masu yawan gaske.

Hakan yasa ya sulale ya dawo gida Najeriya inda anan ne aka kama shi a Abuja a cewar wasu rahotanni.


Like it? Share with your friends!

-1
41 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like