Yan sanda sun ceto wani da aka yi garkuwa da shi


Yan sanda a jihar Benue sun samu nasarar ceto wani dan kasuwa mai shekaru 61 daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi a karamar hukumar Gboko ta jihar Benue.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa mutumin mai suna,John Akombo babban dillaline dake raba kayan kamfanin Nigeria Brewery an kuma sace shi ne a ofishinsa aka tursasa masa shiga cikin wata mota kirar Honda.

Amma shedun gani da ido sun bayyana cewa anyi gaggawar sanar da jami’an yan sanda tawagar inda tawagar jami’an tsaro da suka hada da sojoji suka bi sawun masu garkuwar inda suka ci karfinsu akan titin JS Tarka.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce bayanan da jama’a suka bayar cikin sauri ta taimaka gaya wajen ceto mutumin.

Anene ta kara da cewa jami’an tsaro na ciki gaba da bincike gandun dajin dake yankin domin kama masu garkuwar da suka bar motar su suka tsere.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like