Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami’an ‘yan sanda sun kubutar da biyu daga cikin daliban makarantar sakandaren Bethel Baptist da aka sace a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

A ranar 8 ga watan Yuli, ‘yan bindiga suka far wa makarantar wacce ke karamar hukumar Chikun, suka yi awon gaba da dalibai sama da 100.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, a daren Laraba ‘yan sanda sun ceto biyu daga cikin su a yankin Rijanna da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hukumomin tsaro a jihar sun ce an kai daliban wani asibitin ‘yan sanda don a duba lafiyarsu.

Kubutar da karin dalibai biyun, na nufin an yi nasarar ceto dalibai uku kenan.

A makon da ya gabata, ‘yan sanda sun kubutar da daya daga cikin daliban a wani daji kamar yadda Channels ya bayyana.

Tun gabanin hakan, ‘yan bindigar da suka sace daliban, na neman a biya kudin fansa naira miliyan 60.

Kaduna ta kasance daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ke garkuwa da dalibai da sauran jama’a.

A ‘yan watanni baya-bayan nan an sace dalibai a makarantar koyar da ilimin kula da gandun daji, da jami’ar Greenfield da kuma kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli duk a jihar ta Kaduna.

A makwanbciyarta jihar Neja, ‘yan fashin dajin na rike da daliban Islamiyya sama da 100 da suka sace a garin Tegina.