‘YAN SANDA SUN BUDE WUTA KAN MABIYA SHI’A MASU ZANGA ZANGAR A SAKI ZAKZAKY A ABUJA


A cigaba da fita zanga-zanga da Mabiya Shi’a Almajuran Sheikh Zakzaky keyi kullum a Abuja domin neman gwamnati Nijeriya data saki Malamin nasu Sheikh Ibraheem Zakzaky wanda yake tsare sama da shekaru sannan yake fama da matsananciyar jinya.

Lamarin ya auku ne yau a majalisar dokokin Nijeriya yayin da ake kokarin gudanar da zaman ta yau Talata, wanda hakan ya tilasta musu dage zaman zuwa gobe Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mabiya Shia biyu aka kashe yayin bude wuta sannan aka raunata da dama.

A gefe daya kuma, an zargi ‘yan shi’a da bindige jami’an ‘yan sanda uku a bakin zauren majalisar Tarayyar Nijeriya, inda daya daga cikin ‘yan sandan ya mutu, sauran biyun an garzaya da su Asibiti.

‘Yan Shi’ar suna yunkurin karya kofar shiga majalisar ne dai, yayin da jami’an tsaro suke tare su.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like