Yan sanda a Sokoto sun tabbatar da sace wani dan majalisar dokokin jihar


Yan sanda a jihar Sokoto sun tabbatar da sace, Alhaji Aminu Bodai mamba a majalisar dokokin jihar da wasu yan bindiga suka yi a kauyen Bodai dake karamar hukumar Dange- Shuni ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Abubakar Saqiq shine ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN faruwar lamarin a Sokoto ranar Alhamis.

Bodai mamba ne a jam’iyar APC dake wakiltar karamar hukumar Dange/Shuni.

Sadiq ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin ta bakin baturen yan sanda na yankin.

Ya ce da safiyar yau ne yan bindigar suka je gidan dan majalisar inda suka sace shi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like