Yan sanda a Rivers sun fara farautar mutanen da suka sace abokan aikinsu biyu


Rundunar yan sandan jihar Rivers ta ce ta kaddamar da farautar neman jami’anta biyu da wasu yan bindiga suka sace a karamar hukumar Andoni dake jihar.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindiga sun sace yan sandan biyu a Ngo dake karamar hukumar Andoni.

An ce yan bindiga sun dauke yan sandan ya zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,DSP Nnamadi Omoni ya bayyana cewa ” Zan iya tabbatar maka da faruwar lamarin kuma mun kaddamar da farautar yan bindiga,”

Jihar Rivers na daya daga cikin jihohin Najeriya dake fama da matsalar tsaro

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like