Yan sanda a Kano sun kama mutuminda ya kona wani magidanci tare da iyalinsa


Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama mutumin da ake zargi da kone wani magidanci tare da maidakinsa da kuma karamar yarsu a kauyen Gayawa dake karamar hukumar Ungogo ta jihar.

Bayanin kama daya daga cikin waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa ya fitar.

Sanarwa ta ce bayan samun labarin faruwar mummunan lamarin kwamishinan yan sandan jihar ya bada umarnin kama wadanda suka aikata haka cikin sa’o’i 24.

Hakan ya sa tawagar yan sanda daga hedkwatar rundunar da kuma ofishin yan sanda na Zongo suka kama aiki ka’in dana in.

A karshe aka samu nasarar kama babban wanda ake zargi mai suna, Salisu Idris dan shekara 25 mazaunin unguwar tsohuwar Gayawa ta Gabas a karamar hukumar Ungogo a maboyarsa dake karamar hukumar Munjibir.

Ya amsa laifin hada baki da wani da ya tsere domin kona mutumin da iyalinsa bayan da wancan mutumin da ya tsere ya yi masa alkawarin bashi ₦250,000.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like