Yan sanda a jihar Imo sun kashe mutane uku masu garkuwa da mutane


Jami’an yan sanda a jihar Imo sun samu nasarar bindige wasu masu garkuwa da mutane su uku tare da ceto mutane 7 da suke tsare da su a Dajin Lille dake karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar.

A cewar mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,SP Orlando Ikeokwu kwamishinan yansandan jihar, Rabi’u Ladodo shine ya jagoranci runduna ta musamman karkashin shirin Puff Adder na kakkabe bata gari da ta kai ga ceto mutanen.

Mai magana da yawun rundunar ya ce a yayin samamen kwamishinan ya samu rakiyar kwamandodin rundunar da dama da suka hada da mataimakin kwamishina mai lura da ayyuka ya kara da cewa an samu kayayyakin da dama a dajin da bata garin suka mayar da shi maboyarsu

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like