Yan nPDP sun kafa sabuwar jam’iyyar APC


Yayan jam’iyar APC da suka fito daga jam’iyar PDP da akewa lakabi da nPDP sun balle daga jam’iyar APC inda suka kafa bangare mai suna rAPC ko kuma Reform APC a turance.

Sabuwar jam’iyar ta APC na karkashin shugabancin Buba Galadima tsohon na hannun daman shugaba Buhari kuma makusancin sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a yanzu.

A ranar Laraba Galadima wanda tsohon dan kwamitin amintattun jam’iyar APC ne ya jagoranci ya sauran yan jam’iyar wajen kafa sabuwar jam’iyyar ta rAPC.

A jawabinsa na farko Galadima ya bayyana gwamnatin Buhari a matsayin gagarumar masifa ga Najeriya.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jam’iyar ta gudanar da babban taronta inda aka zabi sabbin shugabanni.

Masana da dama na ganin cewa yan san sabuwar PDP sun yi hakane domin sharewa sauran yan jam’iyar hanya da za ta basu damar sauya sheka ya zuwa jam’iyar da suke so.

Tsarin mulkin Najeriya bai bawa yan majalisar tarayya damar sauya sheka ba har sai an samu rikicin shugabanci a jami’yar su.


Like it? Share with your friends!

1
83 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like