Yan Najeriya Sun Kasa Gane Ayyukan alkhairin Da Buhari Yayi Musu – Lai Mohammed


Alhaji Lai Mohammed ya bayyana nadamarsa guda ɗaya da yake a matsayinsa na minista.

A cewarsa, nadamar tasa bai wuce yadda wasu ƴan Najeriya ke ƙin yabawa gwamnati duk da irin namijin ƙoƙarin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke yi da ɗan abin da ke a hannunsa.

Lai Mohammed, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja.

Ya ce duk da ƙarancin kuɗaɗe, babu gwamnatin da ta taɓa kafa tarihin gwamnatin Buhari a gwamnatocin baya a Najeriya.

Musamman wajen ƙirƙiro tsare tsare da shirye-shirye da zasu kawar da talauci tsakanin mabuƙata da mata har ma da samar da ayyukan yi ga matasa.

Ministan ya ce nadamarsa ita ce wasu ƴan Najeriya sun gaza yaba ƙoƙarin da gwamnatin ke yi, amma suna murna da abubuwan da ba dai-dai ba.

Babbar nadamata a wannan gwamnatin shine ƴan Najeriya sun gaza yabawa abubuwan da gwamnati ke yi da kuɗaɗe ƙalilan.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Hi there to every body, it’s my first go to see of this website; this webpage consists
    of awesome and actually good material in favor of visitors.

    Also visit my web page – FO6QR4gBhg

You may also like