Wannan na zuwa ne lokacin da matsalar ke kara ta’azzara duk da matakan da hukumomi ke dauka na shawo kan lamarin.

Matsalar rashin tsaro a Najeriya ta na ci gaba da kure tunanin yan kasar saboda kasancewar duk yunkurin da ake yi na magance ta tamkar suna tashi ne a banza.

Yanzu matsalar ta kai har yan bindiga sun fara harbe jiragen yakin kasar kamar yadda hedikwatar tsaro ta fitar da wani bayani na jirgin da harbin yan bindiga yayi sanadiyar faruwar sa a jihar Zamfara.

Irin wadannan abubuwan da ke gudana yasa wasu ‘yan kasar ke ganin wadannan matsalolin idan ba’a kara mayar da himma ba zasu iya tarwatsa Najeriya.

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal na cikin masu irin wannan ra’ayin. Ya ce ga dukkan alamu, manufan ‘yan bindigan shine su ga sun hana noma da dukkan al’ammuran kasuwanci.

Shugaban majalisar koli akan lamurran addinin musulunci a Najeriya mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya jima yana kira ga gwamnatin Najeriya kan kara kokari wajen maganin wannan matsalar.

Suma al’ummomin yankunan da wannan matsalar ta yi katutu sun baiwa hukumomi shawarwari musamman ganin cewa karancin jami’an tsaro da ake kai yankunan su na taka rawa ga ta’azzarar matsalolin kamar yadda wani mazaunin yankin Sabon Birni da ke gabascin Sakkwato Abdullahi Muhammad Tsamaye ya fadi wa Muryar Amurka.

Yanzu dai fatar ‘yan Najeriya bata wuce ganin an samu mafita daga wadannan matsalolin ba, abinda yasa suke addu’a domin samun biyan wannan bukatar wadda zata ceto kasar daga halin da ta fada.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti: