Wasu yan Najeriya a Afrika ta Kudu sun gudanar da zanga-zanga kan kama Sowore


Wasu yan Najeriya dake zaune a kasar Afrika ta Kudu sun gudanar da zanga-zangar neman hukumar tsaron farin kaya DSS ta sako Omoyele Sowore.

Hukumar ta DSS ta kama Sowore a birnin Legas ranar Asabar bisa laifin shiryawa da kuma jagorantar zanga-zangar juyin juya halin a fadin kasa baki daya karkashin wata kungiya da ya yi wa lakabi da #Revolutionnow.

Daga bisani an sauya inda ake tsare da shi ya zuwa birnin tarayya Abuja.

Jami’an yan sanda sun ce an kama Sowore ne saboda ya wuce gona da iri.

Zanga-zangar ta gudana ne a ofishin jakadancin Najeriya dake babban birnin kasar Pretoria.

Jagorar masu zanga-zangar, Doris Ikeri-Solarin ta ce basa cikin farin ciki saboda halin da ake ciki a gida.

Sun bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin Sowore da kuma sauran yan kungiyar da suke tsare a hannun yan sanda.


Like it? Share with your friends!

1
94 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like