Yan Najeriya 1500 ne ke zaman gidan yari a kasar Italiya


Stefanou Pontesilli, jakadan kasar Italiya a Najeriya ya ce akalla yan Najeriya da ba su gaza 1500 ne suke zaman gidan yari a kasar.

Pontesilli,ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da yan jaridu a birnin tarayya Abuja.

“A Italiya muna da yan Najeriya kusan 1500 da suke zaman gidan yari adadin mai ya wa ne,” ya ce.

“Wasu lokutan muna turo su gida Najeriya da zarar sun kammala zaman gidan yarin.

Amma ya musalta cewa wasu lokutan kasar Italiya na mayar da yan gudun hijira daga Najeriya zuwa kasar Libiya.

“Bamu taba tura ko wa ba, ko mutum daya ne zuwa Libiya.Wasu yan Najeriya sun makale a Libiya ne saboda sun kasa tsallakawa kasar Italiya amma dukkanin wadanda suka isa Italiya babu wanda, ko da mutum daya ne da aka komar da shi,”ya ce.

“Dukkanin yan Najeriya da suka isa Italiya kuma suke bin doka yadda ya kamata basu da matsala.”

Jakadan ya ce dangantaka tsakanin Najeriya da Italiya na nan da karfinta.


Like it? Share with your friends!

-2
91 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like