Yan majalisar wakilai biyu sun fice daga jam’iyar APC


Jam’iyar APC mai mulki ta rasa mambobinta guda biyu a majalisar wakilai ta tarayya bayan da suka sanar ficewarsu daga jam’iyar.

Yan majalisar sun sanar da ficewarsu daga jam’iyar cikin wata wasika da kowannensu ya aikewa zauren majalisar da kakakin majalisar Yakubu Dogara ya karanta a zaman majalisar na ranar Laraba.

Babatunde Kolawale daga jihar Ondo cikin wasikar da ya aikewa majalisar ya sanar da komawa jam’iyar PDP.

Amma kuma Munkaila Kazzim da ya fito daga jihar Ogun bai sanar da sabuwar jam’iyyar da ya koma ba.

Dukkannin yan majalisar biyu cikin wasikun nasu sun bayyana rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani a matsayin dalilinsu na sauya shekar.

Kazzim ya bayyana cewa siyasar uban gida ta taka muhimmiyar rawa wajen zaben yan takarar da za su wakilci jam’iyar a zaben shekarar 2019.


Like it? Share with your friends!

-1
70 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like