‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Sun Kammala Taro Kan Ka’idojin Aiki Da Dokar ‘Yancin Sarrafa Kudade
Sai dai shugaban majalisar dokokin ta jihar Bauchi Hon. Abubakar Sulaiman wanda kuma shine ke jagorantar kungiyar shugabannin majalisun dokoki ta jihohin Najeriya ya ce ya zuwa yanzu jihohi 10 ne kawai suka fara aiki da dokar daga cikin 36 na kasar.

Batun aiwatar da wannan doka shi ne babban kalubalen dake gaba bayan kwashe shekaru da dama ana gwagwarmaya, wadda ta rinka samun tirjiya daga bangaren gwamnoni, kuma daga bisani an samu nasara.

Hon. Abubakar Sulaiman shugaban kungiyar shugabannin majalisun dokoki na jihohin Najeriya kuma shugaban majalisar dokoki ta jihar Bauchi ya ce jihohi kamar Legas da Delta sun fara amma wasu suna jan kafa saboda matsalolin wajen aiwatarwa. Kuma suna sa ido akan harkokin.

Sai dai masana kimiyyar siyasa dake sharhi kan harkokin demokaradiyya na ganin akwai hakkin akan dukkanin majalisun jihohin su hanzarta samar da dokar kula da sarrafa kudaden su kuma gwamnoni su rattaba hannu akan dokar, kamar yadda Malam Kabiru Sa’idu Sufi ya ce.

To ko wane irin tasiri wannan ‘yancin samun kudade ga ‘yan majalisar dokoki zai yi ga makomar rayuwar al’uama?

Malam Kabiru Sa’idu Sufi wani masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, ya ce ana ganin ce wa samun ‘yancin kai me game da abubuwa da dama musamman wadanda za su taimaka wajen yin dokoki masu inganci da suka shafi ‘yan kasa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.