Yan majalisar dokoki 6 sun koma jam’iyyar PDP


Yan majalisar dokokin jihar Imo su 6 da suka fito e daga jam’iyu daban-daban sun sauya ya zuwa jam’iyar PDP.

Yan majalisar sun sanar da sauya shekar tasu ne cikin wata wasika da suka aikewa kakakin majalisar wacce akawun majalisar ya karanta ya yin zamanta na farko a ranar Litinin.

Biyar daga cikin su sun fice ne daga jam’iyar AA yayin da na shidan su ya sauya sheka daga jam’iyar APGA.

Yan majalisar da suka sauya sheka daga AA zuwa PDP su ne: Mike Ihenatu, Victor Onyewuchi,Ken Agbim, Lloyd Chukwuemaka,Bruno Okoha.

Chidi Collins shine dan majalisa daya tilo da ya sauya shekare daga jam’iyar APGA.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like