Dubban mutane ne ke cigaba da yin kaura daga yankin Tigray na kasar Ethiopia ya zuwa kasar Sudan dake makotaka da su.

An dai shafe kwanaki ana gwabza kazamin fada tsakanin dakarun sojan kasar ta Ethiopia da kuma na kungiyar TPLF dake yankin.

Firaministan kasar ta Ethiopia ya sha alwashin cigaba da farmakin soja har sai dakaru da kuma jami’an gwamnatin yankin sun mika wuya.