Yan jaridu uku sun samu raunin harbin bindiga a wurin taron jam’iyyar APC


Yan jaridu uku da suka fito daga kafafen yada labarai daban-daban sun jikkata bayan da rikici ya rutsa da su a wurin kaddamar da yakin neman zaben dantakarar gwamnan jihar Lagos a jam’iyar APC, Babajide Sanwo-Olu.

An tabbatar da cewa yan jaridun sun samu nau’in raunuka daban daban sakamakon harbin bindiga.

Cikin wadanda abin ya shafa akwai Editan Bangaren Siyasa na jaridar The Nation, Emmanuel Oladesu, wakilin jaridar News Telegraph, Temitope Ogunbanke da kuma mai daukar hoto na gidan talabijin din Ibile.

Da yake bayanin abinda ya faru Ogunbanke ya bayyana cewa yayi sa a da ya samu karamin rauni a kumatunsa duk da cewa an harbe shi a ciki.

“Na tsira daga harsashi biyu a fuskata da kuma cikina daya daga cikin harsashin ya karceni a fuska shiyasa aka saka min filasta,”ya ce.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like