‘Yan Jam’iyyar Democrat Sun Maka Donald Trump A Kotu


‘Yan jam’iyyar Democrat a majalisar dokoki ta tarayya sun shigar da kara a gaban kotun tarayya suna zargin shugaba Donald Trump da laifin karbar kudi daga kasashen waje da sunan kamfanoninsa, abinda ya saba ma tsarin mulkin Amurka.

Wannan karar da ‘yan jam’iyyar Democrat fiye da 190 daga majalisar wakilai da ta dattijai suka shigar, ta yi zargin cewa shugaban ya keta wani sashen da ba kasafai aka san da shi ba na tsarin mulkin Amurka, wanda ya haramtawa duk wani wanda yake rike da wani mukami na gwamnati a Amurka karbar kyauta ta kaya ko kudi daga duk wata kasar waje sai dai idan majalisar dokoki ta yardam masa da hakan kafin nan.

Kafin ya shiga takarar kujerar shugabancin Amurka, Trump dan kasuwa ne na kadarori wanda ya mallaki hotel-hotel da wasu gine-ginen dake dauke da sunansa a kasashe dabam dabam.

A bayan da ya zama shugaban kasa, ya mika aikin gudanar da harkokin kasuwancinsa ga manyan ‘ya’yansa mazaje biyu, Donald Junior da Eric, amma kuma yana ci gaba da rike kamfanonin a zaman nasa.

Wannan ita ce kara ta biyu da aka shigar da Trump game da harkokin kasuwancinsa tun hawansa kan mulki a watan Janairu. 

A ranar litinin ta wannan makon, atoni-janar na Jihar Maryland da na  Gundumar Colombia sun shigar da shugaban kara a kotu suna zargin cewa yana amfani da kujerar shugaban kasa domin arzuta kansa.

Comments 0

Your email address will not be published.

‘Yan Jam’iyyar Democrat Sun Maka Donald Trump A Kotu

log in

reset password

Back to
log in