Yan gudun hijira sun gudanar da zanga-zanga kan karancin abinci


Mazauna sansanin yan gudun hijira dake kan titin Gubio a Maiduguri sun gudanar da wata zanga-zanga ranar Alhamis kan karancin abinci da kuma sauran kayayyakin tallafi da ake samarwa a sansanin.

Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta jawo dakatarwar zirga-zirgar a baben hawa ta tsawon sa’o’i da dama akan hanyar Baga- Maiduguri da kuma Gubio-Maiduguri.

Sansanin na dauke da yan gudun hijira da suka kai 10,000 da suka fito daga kananan hukumomin Marte,Gubio,Kukawa, Kala-Balge da kuma Gwoza.

Mutanen dake sansanin sun kwarara kan titunan biyu inda suka bukaci a mayar da su garuruwansu sun gwammace Boko Haram su kashe su da su zauna sansanin yan gudun hijira dake Maiduguri yunwa ta kashe su.

Wata dake zaune a sansanin mai suna Zara Alhaji Dauda dake da yaya 7 a tattaunawar da tayi da wakilin jaridar Daily Trust ta yi zargin cewa ƴaƴanta biyu ne suka mutu a sansanin sanadiyar yunwa.


Like it? Share with your friends!

-2
83 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like